Hukumomin zabe na Junhuriyar demokradiyar Congo sunce a yau Alhamis ne zasu bada cikakken sakamakon zaben shugaban kasan da aka yi, koda yake ana sa ran bada sakamakon kuma zai tado rigingimmu sosai.
Bayan jinkirin kwannaki biyu da aka samu, wanda kakakin hukumar zaben, Matthieu Mpita yace an fuskanta saboda matsalar kayan aiki, yanzu hukumar na shirin ta bada wannan sakamakon da misalign karfe shida na yammacin yau agogon Congo din.
Sakamakon da aka samu daga kashi casa'in bisa dari na dukkan rumfunan zaben da ya shigo hannu a yanzu na nuna cewa shugaba mai ci yanzu, Joseph Kabila ya kama hanyar lashe zaben da kusan sittin bisa dari na dukkan kuri’un da aka jefa, yayinda babban abokin takaran shi Etienne Tshekedi ke da talatin da uku bisa dari na kuri’un.
A yanzu dai Kinshasha, babban birnin Congo din tsit yake, to amma daman magoya bayan duka jam’iyyun biyu sunce zasu tada masifar rigima idan ba dan takaransu ya ci zaben ba. Kan haka ne yanzu hakan an sa sojoji suka warwatsu ko ina, suna zaune cikin shirin ko da wani tashin hankali zai barke, ayyinda Majalisar Dinkin Duniya ke kira akan wa’anda abin ya shafa da su natsu.