Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saura Shekara Guda Duniya Ta Kare?


Hoto daga wani fim da aka yi kan 'yan kabilar Maya da kuma irin ilmin da suka mallaka, wanda ya kai na mutanen zamanin yau, game da taurari, abinda ya ba su damar iya rubuta kalandar abubuwan da suka faru a baya, da kuma hasashen abubuwan da ka iya faruwa
Hoto daga wani fim da aka yi kan 'yan kabilar Maya da kuma irin ilmin da suka mallaka, wanda ya kai na mutanen zamanin yau, game da taurari, abinda ya ba su damar iya rubuta kalandar abubuwan da suka faru a baya, da kuma hasashen abubuwan da ka iya faruwa

Yau aka fara lissafin kwanakin da suka rage kafin 21 Disamba 2012, ranar da 'yan kabilar Maya suka yi hasashen duniya zata kare

Yau laraba, saura shekara daya cif kafin ranar 21 ga watan Disambar 2012, ranar da mutane da yawa suka yi imanin cewa 'yan kabilar Maya na zamanin jahiliya sun yi hasashen cewa ita ce karshen duniya.

Amma maimakon zaman makoki ko yin wasu abubuwan da za a tsammaci mai tsammanin mutuwa da yi, an yi shirya yin bukukuwa ne na tsawon shekara guda a yankin Kudu Maso Gabashin kasar Mexico, inda nan ne tsakiyar Daular Maya a zamanin jahiliyya.

Hukumar kula da yawon shakatawa da bude ido ta kasar Mexico, ta ce a cikin shekara guda mai zuwa, tana sa ran mutane har miliyan 52 ne zasu ziyarci yankunan Chiapas, Yucatan, Quintana Roo, Tabasco da Campeche na kasar.

Wai ta yaya aka yi 'yan kabilar Maya suka yi hasashen karshen duniyar? Wai ma da gaske ne sun ce karshen duniya zai wakana a ranar 21 ga watan Disambar 2012?

Daular Maya, wadda ta yi tashe da fice daga shekara ta 300 zuwa shekara ta 900 bayan haihuwar Annabi Isa (AS), daula ce da ta mallaki masana ilmin taurari da lokaci fiye da kowace daula ta duniya a lokacin.

Daular Maya tana da kalanda wadda ta faro daga shekarar 3,114 kafin haihuwar Annabi Isa (AS), kuma a karkashin wannan kalanda, ana lissafa shekaru kimanin 394 a matsayin Zamani guda, ko Baktun a harshen kabilar Maya. Lamba "13" tana da matukar muhimmanci ga kabilar Maya, kuma sun rubuta cikin kalandarsu cewa Zamani, ko Baktun, na 13, zai zo karshe a ranar 21 ga watan Disambar 2012.

Hasashen cewa wannan rana ita ce karshen duniya ya samo asali daga wani dutse mai rubutu da aka gano cikin shekarun 1960, a lokacin da ake tonon wani wurin da aka taba yin wani gari na kabilar Maya a Jihar Tabasco, wanda a jiki aka ruybuta cewa wani gunkin da suke bauta ma zai komo duniya a karshen Zamani ko Baktun na 13.

Labaran wannan abu sun kara bazuwa kamar wutar daji a Internet a bayan da Cibiyar Ayyukan Tone-Tonen Wuraren Tarihi ta kasar Mexico, ta bayarda sanarwar cewa ta gano wani tubali mai magana kan wannan rana ta 12 ga watan Disambar 2012 a wasu wuraren tsoffin garuruwan Daular Maya da aka tono.

Sai dai kuma, duk da ilmi da aka ce 'yan kabilar Maya sun mallaka fiye da na kowace al'ummar duniya a wancan lokacin, masana da yawa sun yi nuni da cewa akwai rubuce-rubucensu da suek magana kan wasu abubuwan da zasu faru bayan wannan rana ta 21 ga Disambar 2012, kuma idan har duniya zata kare daga wannan lokacin, to ai ba zasu yi karin rubutun ba.

Haka kuma, wasu masanan sun ce da ma haka bil Adama yake, ruruta mummunan abu, tare da kaskantar da wani abu na alheri ko yin oho da shi.

Wasu kuma, cewa suka yi ai 'yan Maya sun ce karshen Zamani ne zai zo, ba su ce karshen duniyar ba, kuma a lissafinsu, Zamani da yawa ya zo ya shige.

Allah dai kadai Y bar ma kansa sani.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG