Lahadi idan Allah ya kaimu za’a yi zaben wakilan Majalisar wakilai a karon farko tun cikin fiye da shekaru goma.
Ana sa ran cewa jam’iyar shugaba Alassane Ouattara ta Democratic itace zata lashe yawancin kujeru. Haka kuma, kila kiran da magoya bayan tsohon shugaba Laurent Gbagbo suka yi cewa a kauracewa zaben zata taimakawa kawancen Mr Ouattara,
A tarzomar da aka yi kafin zaben na gobe, jami’an kasar sunce mutane uku aka kashe, wasu uku kuma suka ji rauni a ranar Laraba a lokacinda aka aka harba roka a yankin Grand Lahou kafin mohaya bayan shugaba Ouattara suyi wani gangami. Idan ba’a mance ba, an rantsar da shugaba Ouattara bayan da magoya bayansa suka kama tsohon shugaba Gbagbo.