Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

John McCain Ya Soki Gwamnatin Najeriya


Dan Majalisar Dattawan Amurka, Senata John McCain daga Jihar Arizona.
Dan Majalisar Dattawan Amurka, Senata John McCain daga Jihar Arizona.

A wannan lokaci da duniya take zuba idanu domin gani hukumomin Najeriya tare da agajin kasashen turai sunyi kokarin ceto daliban Cibok, 'yan siyasa har yanzu bakinsu bai bar kumfa ba, saboda Senata John McCain daga Amurka ya nuna fusatarshi akan gwamnatin Najeriya da ta bari aka sace dalibai.

Da yake magana da babban gidan talabijin na MSNBC a baya-bayannan, Senatan daga Jihar Arizona yayi amfani da kalmomi masu karfi wajen kwatanta lamarin Cibok.

John McCain yace "babu lafazin da zan iya amfani dashi wajen nuna irin cin mutuncin da sace daliban nan ya nuna. A tunanina, mu aika na'u'rorin bincike, ko me gwamnatin Najeriya take yi, ya kamata mu hada kan duk wasu na'u'ro'ri da muke dasu, wasu na sama, wasu na ruwa, da ma tauraron dan adam, da kuma jirage marasa matuka a ciki, mu aika domin nemo wadannan yara."

"Sannan kuma mu gayawa gwamnatin Najeriya cewa wannan lamari na Cibok, 'cin mutuncin duka bil adama ne', da duk akidun duniya. Zamu yi wani abu akai, kuma muna gani ya kamata ku bamu hadin kai," a cewar Senata McCain.

Senatan bai tsaya anan ba, saboda yayi tsokaci akan sojojin Najeriya.

"Sojojin Najeriya kamar yadda kowa ya sani, babu abunda zasu iya yi. Wannan karan abun ya lalace da za'a iya kiranshi "ta'asa". Dole muyi wani abu, mu da kasashen dake kawance da mu. Nayi imanin cewa muna da kayan aikin taimakawa", inji John McCain.

"Baza'a amince da wannan a kowani karni ba, balle wannan na 21".

Yanzu dai an share kusan makonni hudu kennan da sace daliban mata, wadanda har yanzu ba'a san inda suke ba. Sojojin Najeriya a baya sunce sun ceto kusan duka daliban, amma daga baya suka janye kalamunsu.

A baya-bayannan ma, Shugaba Jonathan ya fito akan kafar Talabijin yace shima bashi da tabbacin adadin yaran, balle ma inda suke.

Daliban su kusan 300 suna rubuta jarrabawarsu ta karshe ne, na fita daga Sakandare a lokacin da 'yan bindigan suka kaiwa makaransu farmaki, suka zuba su a cikin motoci suka tafi dasu.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG