Hannatu Musawa ta cigaba da bayani akan kashe-kashen da yaki karewa a arewacin Najeriya.
“Kashe-kashennan, anayi ba tun yau ba, wannan meyasa ya zama daban? Dauke yara? Kashe yara? Ai kafin a dauke wannan dari biyun, akwai 35 da aka dauke. Abun na ban mamaki da har yanzu naji shiru, ba’a ma fara maganar wannan ba.” A cewar Musawa. “Wannan abunda yasa ya zama daban, saboda turawa, sun dauki nauyin wannan abun, har suna maganarshi, shine ya saka manyanmu da shuwagabanninmu suka ji kunya, ya zama musu dole su fito. Saboda borin kunya ne, saboda duk duniya ta saka musu ido, ance meyasa basuyi magana ba.”
Hannatu ta fitar da wani kalubale “tsoron da muke ji, idan yau anje ance an gama da batun yarannan, an dawo da yarannan, wai shin maganar kennan ta kare? Za’a ce ba wani matsala? Ai matsalar na nan, cutar da ke cinmu tana nan, ba’a nemi maganinta ba. Kuma maganinta dole-dole, idan ma an gama da batun yarannan, an dawo da dasu wajen iyayensu, to yakamata mu san abunda muke ciki. Wannan babu mai gyara mana shi, sai mu.”
Lamarin Cibok ya fallasawa duniya irin rashin tsaro dake addabar jama'ar arewacin Najeriya, musamman yadda kungiyoyin kasa da kasa suke fahimtar cewa gwamnati nada masaniya akan hare-hare, amma sai ta kawar da kai, bisa rahoton kungiyar Amnesty International, mai kare hakkin bil adama.
Asabar dinnan, Kungiyar Gwamnonin Arewa ta shatawa shugaba Jonathan watanni 3 domin kawo karshen tashe-tashen hankula a Najeriya, sama da kwanaki 26 kennan da sace dalibai mata su kusan 300.