Kungiyar Amnesty ta ce ta tabbatar ta hanyoyi da dama cewa tun karfe 7 na maraicen 14 Afrilu, hedkwatar sojoji dake Maiduguri, da kuma rundnar sojan dake garin Damboa, kilomita 37 daga Chibok, sun samu labari daga majiyoyi da yawa cewa ga 'yan bindiga sun doshi garin Chibok. Wasu manyan hafsoshin sojan Najeriya biyu sun gaskata wannan labarin in ji Amnesty.
Amma sai aka bar sojoji kwaya 17 dake Chibok kawai da 'yan sandan garin suka yi fada da wadannan 'yan bindiga ba a kai musu dauki ba. Su kuma da aka fi karfinsu, suka ja da baya.
A kwanakin baya, wani sojan Najeriya wanda ya tattauna da Sashen Hausa na Muryar Amurka, ya zargi da hannun manyan sojoji a hare-hare da ake ta kaiwa a arewa maso gabashin Najeriya, inda ma yace akwai sojojin Najeriya dake yiwa Boko Haram aiki, suna kashe 'yan uwansu sojoji.