Kwana daya kafin Amurkawa su yi bukukuwan Ranar Uwa a yau lahadi, mai dakin shugaban ta rike masa wajen gabatar da jawabinsa na mako-mako ga al’ummar kasa, inda ta bayyana jimami ga iyayen ‘yan mata su 276 wadanda har yanzu sun a hannun wadanda suka sace su.
Ta ce, “Ni da Barack, muna ganin wadannan yara da aka sace kamar ‘ya’yanmu mata su biyu. Irin halin bakin ciki da tashin hankalin da iyayensu ke ciki a wannan lokaci, sai dai kawai mutum yayi tunaninsa.”
Har ila yau, uwargidan shugaban ta soki lamirin kungiyar ta’addanci ta Boko Haram da ta sace ‘yan matan. Shugaban ‘yan Boko Haram din yace sun a da niyyar sayar da ‘yan matan a zaman bayi.
Wannan mummunan aiki na rashin imani, ya faru ne a hannun kungiyar ta’addanci mai neman hana wadannan ‘yan mata samun ilmi in ji uwargidan shugaban.
Michelle Obama ta kara da cewa, “ina son ku sani cewa Barack ya umurci dukkan sassan gwamnatinmu da su yi duk abinda zasu iya domin tallafawa gwamnatin Najeriya wajen samowa da maida wadannan ‘yan mata zuwa gidajensu.