Yayin da ya rage ‘yan kwanaki ya bar fadar White House, a jawabinsa na ban kwana na yammacin jiya Laraba Shugaba Joe Biden ya fitar da wani gargadi game da abin da ke tafe a nan gaba sannan ya bukaci a gudanar da mahimman sauye-sauye a kundin da aka assasa kasar akai.
Shugaban Amurka mai barin gado ya yi amfani da damar wajen yin gargadi ga al’ummar kasar, kamar yadda Dwight Eisenhower ya yi a 1961 sa’ilin daya bayyana damuwa game da “kamfanonin kera makamai” a jawabinsa na ban kwana.
Biden ya bayyana cewa “salon mulkin ‘yan tsiraru na kara kankama a Amurka” kasancewar an tattara iko da kudade a hannun wasu mutane kalilan.
Ya kuma caccaki “kamfanonin fasaha” da dandalin sada zumunta, inda yace ana cakuda gaskiya da karya domin samun mulki da riba.”
Ya bukaci kasar ta ci gaba da yakar matsalar sauyin yanayi, yana cewa, “kada mu bari ayi mana barazana mu sadaukar da makomarmu.”
Biden ya yi amfani da jawabin wajen sanar da shawarar da yake da matukar buri akai.
Ya na bukatar ayi gyara a kundin tsarin mulkin Amurka “domin fayyace cewa babu wani shugaban kasa da ke da kariya daga laifuffukan da ya aikata yayin da ya ke kan karagar mulki.”
Dandalin Mu Tattauna