Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Haramta Motoci Masu Dauke Da Fasahar China


CHINA-ECONOMY-TRANSPORT
CHINA-ECONOMY-TRANSPORT

Amurka ta zartar da hukuncin karshe a kan haramta fasahar China a jikin kananan motocin dake kasuwannin kasar, inda take harin na’ura mai kwakwalwa da jikin motocin dake fitowa daga kasa ta 2 mafi karfin arziki a duniya a kan barazanar tsaro.

Sanarwar, wacce ta kuma shafi fasahar kasar Rasha, na zuwa ne a dai dai lokacin da Shugaba Joe Biden ke kammala kokarin da yake yi na kara takure China, bayan daukar tsawon wata guda ana tsara dokoki.

Dokar ta biyo bayan sanarwar da aka fitar a watan da muke ciki na cewa Washington na tunanin a kan sabbin takunkuman da za su magance barazanar da ake fuskanta daga jirage marasa matuka masu dauke da fasahar kasashen abokan gaba irinsu China da Rasha.

Dokar karshe na aiki ne akan ababen hawan fasinja da nauyinsu bai gaza fam 10, 001 ba, a cewar ma’aikatar cinikin Amurka.

Saidai, akwai shiri na fitar da wani hukuncin na daban akan fasahar dake jikin motocin haya irinsu akori kura da bas-bas “nan bada jimawa ba.”

Haramta sayar da motocin zai fara aiki akan wadanda aka kera a 2027.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG