Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biden Ya Sassautawa 37 Daga Cikin Dauraru 40 Da Ke Jiran Kisa Hukuncinsu


Matakin ya rage saura ‘yan tsirarrun da suka aikata munanan kashe-kashe sakamakon kiyayya ko ta’addanci ke fuskantar hukuncin kisa a matakin tarayya-hakan ma an tsawaita jan kafa karkashin mulkin Biden akan aiwatar da hukuncin.

A yau Litinin, Shugaban Amurka Joe Biden ya sassauta hukuncin da aka zartarwa 37 daga cikin daurarru 40 dake jiran kisa, inda ya dauki matakin gabanin dawowar Donald Trump wanda a wa’adin mulkinsa na farko ya tabbatar da hukuncin kisan da aka zartarwa daurarru da dama ta hanyar allurar guba.

Biden dake da kasa da wata guda ya bar mulki, na fuskantar karin kiraye-kiraye daga masu adawa da hukuncin kisa akan ya sassautawa daurarrun dake kiran kisa hukunci zuwa daurin rai da rai ba tare da afuwa ba, hukuncin da daurarru 37 din ke kai a halin yanzu.

Matakin ya rage saura ‘yan tsirarrun da suka aikata munanan kashe-kashe sakamakon kiyayya ko ta’addanci ke fuskantar hukuncin kisa a matakin tarayya-hakan ma an tsawaita jan kafa karkashin mulkin Biden akan aiwatar da hukuncin.

Ragowar daurarru 3 da zasu cigaba da fuskantar hukuncin kisan a matakin gwamnatin tarayyar sun hada da Dzhokhar Tsarnaev, wanda ya taimaka wajen kai harin bam yayin tseren yada kanin wani na 2013, da Dylann Roof, wani mai tsananin kyamar jinsi daya harbe tare da hallaka wasu bakaken fatan 9 dake kan hanyarsu ta zuwa coci a garin Charleston, na Carolina ta Kudu.

Sauran wanda zai cigaba da fuskantar hukuncin kisan shine, Robert Bowers, wanda ya hallaka yahudawa 11 a harin kan mai uwa da wabin daya kai wurin bautar Yahudawa na “Tree of Life Synagogue a garin Pittsburgh, a 2018.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG