Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Neja na Binciken 'Yan Tsattsauran Ra'ayi


Gwamna jihar Neja, Ma'azu Babangida Aliyu.
Gwamna jihar Neja, Ma'azu Babangida Aliyu.

Gwamnatin Jihar Neja ta kafa kwamitin bincike akan wasu masu tsattsauran ra'ayin addini da suka bullo a garin Bida cikin Jihar Neja.

Gwamnan jihar Neja, Dakta Muazu Babangida Aliyu, ya ummarci kwamishinoni masu kula da harkokin addinai da na kananan hukumomin jihar dasu binciki wadansu mutane da ake zargin masu tsattsauran ra’ayin addini ne a garin Bida.

A baya dai gwamnatin jihar ta dauki matakin korar mutanen Darul-Islam daga jihar alamarin da tace yayi tasiri matuka.

Gwamna Babangida Aliyu yace ”sai maganar wadannan ya taso aka ce boko haram ne wannan, yau ya kamata mu tattauna wannan alamari saboda a lokacin da muka tarwatsa ‘yan Darul-Islam, gwamna Bauci ma ya gayami kwanaki cewa ka turo mani mutanen nan addinin da sukeyi daban ne amma tunda basu soma daukan sanda ba na barsu.”

Ya kara da cewa "amma wadannan yanda na samu rahoto lallai nasu addini da bane, kuma inya kaucewa Islam, kuma suna amfani da sunan Islam to yakamata mu samu rahoton bincike da gaggawa, kuma ance ‘yan cikin garin Bida ne."

Gwamnan dai yana bayani ne a gaban tawagar limamain juma’a na jihar ta Neja.

Kwamishinan kula da harkokin addinai na jihar Alhaji Shehu Haruna yace tuni suka fara daukan mataki akan wadannan mutane.

Sakataren majalisar limaman, Sheikh Umar Faruk, yace limaman suna gudanar da ayyuka na hada kan jama’a. Sun kuma yi kira ga hukumomin Najeriya dasu himmatu waje kubuto da ‘yan matan da aka sace.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG