Alhaji Abdulkadir Zailani Ibn Aliyu “Iko sai Allah”, shine shugaban tawagar dattawan “wato abunda yake tafe da mu, shine zancen sarki na Agaye. Bayan sarki ya rasu, idan sarki ya rasu, bayan kwanaki uku ko bakwai, ana sanar da masu zaben sarki. Sannan sunje sunyi zabe, ranar Asabar, kuma idan an yi zabe, bayan kwanaki uku ko hudu, zamu ji wanda yaci zabe. Amma tun ranar da akayi wannan zabe, bamu ji kowani motsi daga gwamnati, kuma ba wani bayanin da muka ji daga kowa.
Shima Alhaji Abdullahi Mai Yaki, shine Dan Galadiman Agaye, yace a tarihin masarautar, ba a taba yin zaben sarki sau biyu ba, “sau daya ne, idan akayi aka tabbatar, dama lokacin da ba maganar gwamnati, tun daga garinmu, za’a nada cewa ga wanda Allah Ya baiwa nasara.”
Mai Yaki ya kara da cewa mutan agaye “ba walwala, babu jin dadi. Mutane bakinsu da kunnuwansu na jiran gwamnati ta bayanna.”
Shi kansa gwamnan jihar Neja, Muazu Babangida Aliyu, yace a matsayinsa na mai yanke hukunci, ba zaice komai sai abunda aka kawo mishi. A halin da ake ciki dai yanzu, ba’a kaiwa gwamnan komai ba.