Gwamna Babangida Aliyu, wanda kuma shine shugaban kungiyar gwamnonin jihohin arewacin Najeriya yace har kwanan gobe sarakuna nada wata daraja ta masamman da ake ganin kimarsu.
Ya kara da cewa ”idan sarauta bata da daraja da yanzu ta fadi, munji ‘yan gurguzun da sun zazaga, amma sun dawo sun runguma, don yau ko Sin da Rasha da suka rusa, suna neman yanda zasu dawo da irin wadannan abubuwa. Ingila ko dake da wayo tunda aka fara basu rusa nasu ba, saboda haka duk wanda ke cewa ai sarauta bata da amfani to shine baida amfani kuma ba zai amfani kowa ba."
Gwamna Babangida Aliyu ya furta hakan ne a lokacin da yake jawabi a fadar mai martaba sarkin Sudan na Kontagora.
Ya kara da cewa kasancewar masarautar ta Kontagora nada iyaka da dajin Birnin Gwari, da kuma jihar Zamfara dake fama da yawan tashe-tashen hankali, a saboda haka akwai bukatar sa ido akan abun dake zuwa da dawowa a yankin.
Shugaban karamar hukumar Kwantagora Nasiru Muhammad yace tuni kanana hukumoni dake masarautar Kwantagora suka fara daukan matakin gudanar da taruruka a tsakanin su da fada.