sa sarakuna a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya ba zasu ci gaba da gudanar da aikin su na ci gaban alumar kasa da kuma tabbatar da zaman lafiya a tsakanin jama’a.
Mai martaba sarkin na Agaye Alhaji Yusuf Nuhu wanda yake zantawa da manema labarai a fadar sa, yace dama aikin sarakuna shine sasantawa a tsakanin jama’a da kuma tabbatar da gani an samu zaman lafiya a kasa.
Sarkin na Agaye yace ”dama muna da abunda yakamata muyi kuma munayi ko a samu ko ba’a samu ba sarakuna sune jama’a suka sani, ko gwamnati, ita ma kanta idan abu ya dagule wa ake nema sarakuna, saboda haka a shirye muke koda wanna lokaci aka zo mana neman a zauna lafiya aikin mune dama jama’a ta muce."
Da yake jawabi akan rikicin Fulani da manoma sarkin yace zai yi iya yinsa domin ganin cewa bagarorin biyu sun sami fahimtar juna a masarautarsa.
Wanna shine karon farko da sarkin yayi magana da manema labarai, tun tabbatar masa da sarautar.
”Na farko ina mika godiyata, masamman ga Subuhanahu wata’ala dakuma wadanda Allah yasa suka taimaka har muka kawo ga wanna matsayi ina masu godiya."