WASHINGTON, DC —
Kimanin makonni biyu kennan, da rasuwar tsohon sarkin na Agaye, Alhaji Muhammadu Kudu Abubakar, bayan share shekaru goma yana mulkin masarautar.
Alhaji Idris Ndako shine sakataren gwamnatin jihar Neja, kuma shine ya bayarda sanarwar sabon sarkin a madadin gwamnati.
“Yau dai Allah Ya sa maigirma gwamnan Neja, Dr. Muazu Babangida Aliyu ya tabbatar da sabon sarki na Agaye, sunanshi kuma Yusuf Nuhu”, a cewar Alhaji Idris.
Sakataren ya kara da bayanna dalilin da yasa aka dauki lokaci kafin a bayanna sabon sarkin “ba wai ana sauri bane, domin idan anyi sauri ana nuna kamar cewa ana sauri ne wani ya mutu.”
Sabon sarkin na Agaye, Alhaji Yusuf Nuhu mai shekaru 65 a duniya, ya taba zama komishina a ma’aikatar yada labarai, a lokacin mulkin soja a jihar Neja, sannan kuma tsohon ma’aikaci a babban bankin Najeriya, wato CBN, kuma yayi ritaya a shekara ta 2008.
Masarautar Agaye dai, na daya daga cikin masarautun jihar Neja guda takwas, masu matsayin daraja ta daya.