ABUJA, NIGERIA - Dama a duk lokacin da a ka samu karin farashin litar man fetur kayan masarufi na kara tsada kuma ko da an samu sauki ba ya sa kayan su sauko.
A lokacin da tsohon Shugaba Buhari ke tsara janye tallafin na man fetur a 'yan watannin karshe na gwamnatin sa; 'yan kasuwa sun yi hasashen in an kawar da tallafin litar za ta koma daga tsakanin Naira 350-400 amma ayyana mafi tsada Naira 557 ya ba mutane mamaki da tunanin in an matsa lamba gwamnati za ta rage mafi tsadar da a ka taba samu a tarihin Najeriya.
To ko da yake a lokacin da Shugaba Tinubu ya ayyana janye tallafin bai fadi lokacin da janyewar za ta fara aiki ba, bayanai sun nuna Majalisa ta sanya kasafi mai tallafi zai kare ne zuwa karshen watan nan na Yuni.
Kungiyar Kwadago da ta janye tafiya yaji za ta dawo tattaunawa da gwamnati ranar 19 ga watan nan,inda a lokacin ne za a iya sanin irin sauki ko rashin sa da za a samu.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya: