Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Janye Tallafin Man Najeriya Ya Janyo Matsaloli Wa Jama'a Da Ke A Kan Iyakar Najeriya Da Jahar Tahoua Ta Nijer


Jarkokin Man Fetur Na Fasa Kwauri Da Hukumar Kwastam Ta Kama A Nijar
Jarkokin Man Fetur Na Fasa Kwauri Da Hukumar Kwastam Ta Kama A Nijar

Faranshin man fetur da a ke tsallakowa da shi daga Tarayyar Najeriya ya yi tashin gwauron zabi a iyakar da ta hada Jahar Tahoua ta Jamhuriyar Nijar da Jahar Sokoto, sanadiyyar janye tallafin man da sabon shugaban kasar Najeriya ya bayyana nan da nan bayan ya sha rantsuwar kama aiki.

Sai dai, masu harakokin sufuri a Nijar da ke shan wannan man a iyaka, ko a rariya ko a tituna sun ce, ba su yi karin kudin dakon fasinja ba a hukumance, sai dai in masu motoci ne a kashin kansu su ka aiwatar da hakan.

A kan iyakar Nijar da Najeriya gefen Birni N'Konni Jahar Tahoua Jamhuriyar Nijar da Illela Jahar Sokoto Tarrayar Najeriya, farashin man fetur na bayan fage da ake amfani da shi a mafi yawan zirga-zirga ya yi tashin gwauron zabi biyo bayan janye tallafin mai da sabon shugaban kasar Najeriya ya bayyana, biyo bayan rantsuwar kama aiki a yan kwanakin da suka gabata.

Amma kuma masu sayar da man fetur na bayan fage da a ka fi anfani da shi a Nijar a iyakar kasar da Tarrayar Najeriya, na cewa abin bai gyaru ba kasancewar tsada ta yi yawa tun daga inda suke sayo shi daga Najeriya.

A cewar shugabannin kungiyoyin sufuri a garin Birnin N'Konni, basu yi karin kudin sufuri ba a hukumance, sai dai, in masu motoci ne suka yi karin kudin a kashin kansu.

Radadin janyen tallafin man fetur, ana iya cewa ya shafi harakokin kai-komo da na aikin yau da kullum da ma ayukan gonaki da na sana'o'i da dama a Jamhuriyar Nijar.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG