Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnonin Najeriya Sun Goyi Bayan Matakin Cire Tallafin Man Fetur 


Tinubu ya gana da wakilan manyan kungiyoyin dillalan man fetur
Tinubu ya gana da wakilan manyan kungiyoyin dillalan man fetur

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kare matakin da gwamnatinsa ta dauka a makon da ya gabata na cire tallafin man fetur, matakin da ya janyo hauhawar farashin kayayyaki da sufuri, a cewar kamfanin dillancin labaran AP.

Tinubu ya roki ‘yan Najeriya da su kara hakuri, yayin da miliyoyin ‘yan kasar ke fuskantar karin matsin tattalin arziki. Kudaden da za a tara bayan cire tallafin man da aka kwashe shekaru da dama ana bada wa, zasu taimaka a kokarin da gwamnati ke yi na yaki da talauci da kuma aiwatar da wasu shirye-shirye, kamar yadda shugaban ya shaida wa gwamnoni a wani taro da suka yi a Abuja, babban birnin Najeriya.

“Muna iya ganin tasirin talauci a fuskokin jama’armu. Talauci ba abin gado ba ne, daga al’umma yake zuwa. Matsayinmu shi ne mu kawar da talauci,” abin da wata sanarwa daga fadar shugaban Najeriya ta ambaci Tinubu na cewa kenan.

Tinubu ya gana da wakilan manyan kungiyoyin dillalan man fetur
Tinubu ya gana da wakilan manyan kungiyoyin dillalan man fetur

Gwamnonin sun goyi bayan cire tallafin man kuma sun yi alkawarin yin aiki tare wajen aiwatar da shirin, a cewar sanarwar fadar shugaban kasar.

Duk da cewa Najeriya kasa ce mai arzikin mai, amma ta dogara ne kan man fetur da ake shigowa da shi daga kasashen waje, kuma gwamnati ta kwashe shekara da shekaru tana bada tallafa kan man.

Tinubu ya gana da wakilan manyan kungiyoyin dillalan man fetur
Tinubu ya gana da wakilan manyan kungiyoyin dillalan man fetur

Sai dai raguwar kudaden shiga daga mai da ke samu a daidai lokacin da ake fama da matsalar satar mai da ta yi yawa da kuma raguwar zuba jari daga kasashen waje, gwamnati ta ce ci gaba da bada tallafin man ba zai yiwu ba. Gwamnati ta ware wa bangaren tallafin mai Naira tiriliyan 4.4 (dala biliyan 9.5) a shekarar 2022, kudin da suka zarta na bangarorin ilimi, kiwon lafiya da ababen more rayuwa idan aka hada gaba daya.

Tinubu ya gana da wakilan manyan kungiyoyin dillalan man fetur
Tinubu ya gana da wakilan manyan kungiyoyin dillalan man fetur

Ko da yake, manazarta sun caccaki shawarar da gwamnati ta yanke ta janye tallafin ba tare da wasu matakai na taimaka wa al’uma ba, musamman a lokacin da ‘yan Najeriya da dama ke fama da rashin ayyukan yi da talauci.

Kungiyoyin kwadago sun yi barazanar shiga yajin aiki domin nuna adawa da matakin cire tallafin amma daga baya suka janye.

Jihohin Najeriya sun fara daukar matakai dabam-dabam don taimaka wa ‘yan kasar, musamman ma’aikatan da ke zuwa aiki a kullum.

A wannan makon jihohin Edo da Kwara sun rage ranakun zuwa aiki a mako daga kwanaki biyar zuwa uku. Wasu jihohin kuma sun ce suna duba yuwuwar kara mafi karancin albashin Naira 30,000 ($65) da ake biya yanzu.

XS
SM
MD
LG