Mataimakin dan takarar shugaban kasa na babbar jam'iyyar hamayya APC, Farfessa Yemi Osinbanjo, yace yanzu Najeriya tana fuskantar manyan kalubale biyu, sune rashin tsaro da kuma cin hanci da rashawa.
Farfessa Osinbanjo, wanda yake magana a lokacin wata ganawa da 'yan kasuwa da kuma shugabannin addinin kirista a jihohin Adamawa da kuma Taraba, yace, ainihi ma cin hanci da rashawa shine ya haifar da rashin tsaro.
Osinbanjo yace, Najeriya zata ci gaba da fuskantar wadannan matsaloli muddin aka ci gaba da yin abunda ake yi ahalin yanzu.
Dan takarar mataimakin shugaban kasar yace wadannan matsaloli zasu bukaci hadin kan dukkan 'yan kasa domin a shawo kansu.
Mataimakin shugaban kasar ya kai wannan ziyara ce a dai dai lokacinda shugabannin kungiyar addinin kirista ta Najeriya reshen jihar Taraba, ta fito ta bayyana goyon bayanta ga shugaban kasa Goodluck Jonathan.
'Yar takarar Gwamna na jam'iyyar APC a jihar Taraba, Senata Aisha Jummai Alhassan, tace dama can ta shirya zata gana da shugabannin addinin kirista da magoya bayansu a jihar, da Farfessa Osinbanjo ya sami labari, yace shima yana so ya gana dasu. Kuma suka hadu suka gana da su.
Ga karin bayani.