Shugaban kawancen jam'iyyun adawa na kasar Nijar ko COPA Alhaji Muhammad Usman shi ya sanya hannu ga wasikar da suka aikawa ECOWAS ranar 9 ga wannan watan.
Cikin wasikar sun bayyana matsalolin da suka yi sanadiyar daukan matakin kauracewa zaben zagaye na biyu wanda za'a yi ranar 20 ga watan da muke ciki.
Alhaji Muhammad Dudu ya yi karin bayani akan lamarin. Yace ba kasawa ba ce ta sa suka dauki matakin, dattaku ne ya sa.Matakin nunin son kasa ne da tausayawa jama'a. Yace kada domin son mulki su bari wani ya saci kuri'unsu ya mulkesu suna ji suna gani. Dalili ke nan suna son kotun koli ta duba koke-kokensu akan magudi da aka tafka da sace-sace a samu a gyarasu. Duk 'yan siyasa kama daga Hamma Ahmadou da sauran da aka tsare saboda dalilan siyasa a sakosu.
Kawancen jam'iyyun na COPA har wa yau a cikin wasikar ya bukaci kungiyar ECOWAS ta warware kiki-kakan dake neman maido da hannun agogo baya a tsare-tsaren zaben zagaye na biyu da zai hada Hamma Ahmadou da Mahammadou Issoufou. A nemi hanyar da ta dace a fidda wa 'yan adawa 'yancinsu.
To amma a ra'ayin jam'iyyar PNDS mai mulki tace rashin sanin tudun dafawa ne shi ne dalilin take-taken 'yan adawa kamar yadda sarkin yakin neman zaben Mahammadou Issoufou minista Uhu Madu Mahammadou ya fada. Yace babu kungiyar ECOWA cikin tsarin zaben Nijar. Abun da 'yan adawa keyi kame-kame ne kawai. Yace cikin wasikarsu sun ce ba daidai ba ne a ce dan takara yana kaso. Sai yace to amma ai tun a cikin kaso ya nemi tsayawa takara. Sakinsa daga gidan kaso baya hannun gwamnati. Yana hannun shari'a ne. Sai su jira sai an yi masa shari'a, abun da kuma ta yanke dashi za'a yi aiki.
A hukumance shugaban kasar na yanzu zai gama wa'adin mulkinsa ranar daya ga watan gobe. Saboda haka dole ne CENI ta gudanar da zaben zagaye na biyu ranar 20 ga watan nan babu fashi.
Ga karin bayani.