Tun watan jiya ne aka fara raderadin bullar cutar sankarao a wasu unguwannin Niamey lamarin da ya sa sakataren ma'aikatan kiwon lafiya da ma'aikata suka kira taron manema labarai domin shaida masu sahihiyar gaskiya dangane da lamarin.
Malam Halaru Sha'aibu na ma'akatar kiwon lafiya ya tabbatar da cewa kwayar cutar sankarao dake yawo cikin kasashen dake makwaftaka dasu ta shigo Nijar. To saidai gwamnati ta kebe wuraren da za'a kula da mutanen da suka kamu da cutar. Wadanda basu kamu da ita ba ana yi masu allurar rigakafi.
Banda wannan matakin an umurci duk likitocin jihohi da sun dinga aiko da rahotannin abun da suka gani domin kaucewa yaduwar cutar.
Hukumomin kiwon lafiya sun ce sun dauki matakan rigakafin yaduwar cutar ta hanyar bada allurar rigakafi a wasu garuruwan yankunan Tawa da Niamey wuraren da cutar ta fi kamari. Tuni aka yiwa dubban mutane allurar.
Kawo yanzu babu wanda ya rasa ransa daga cikin wadanda cutar ta kama.
Ga karin bayani.