Lahadin nan ake sa ran Jam’iyyar ANC a Afirka ta kudu zata kammala shagulgulan da aka shirya a karshen mako, domin murnar jam’iyyar ta cika shekaru dari da kafuwa. Za a kammala shagulgulan ne tareda gangami da jerin gwano karkashin jagorancin shugaban kasar Jacob Zuma.
Shugabannin kasashen Afirka masu yawa ne suka halarci bikin karrama kungiyar kwato ‘yanci da ta fi dadewa a nahiyar, karkashin jam’iyyar ce Nelson Mandela ya shugabanci kasar bayan faduwar tsarin mulkin wariya.
Mr. Mandela bai sami halartar bukukuwan ba sabo da rashin kwari jiki.
Ana gudanar da wadan nan bukukuwan ne a wurin da aka kafa jam’iyyar tun farko a birnin Bloemfontein.
A wani bangare na bukukuwan a daren jiya shugaba Jacob Zuma ya kunna fitilar aci bal-bal a majami’ar da masana da ‘yan gwagwarmaya suka kafa jam’iyyar ANC ranar 8 ga watan janairu 1912.
An kafa kungiyar ce da zummar yaki da nuna banbanci, kuma gagwarmayar ta ce ta kawo karshen mulkin tsirarrun farar fata a Afirka ta kudu a 1994.
Nelson Mandela ne bakar fata na farko da ya shugabanci kasar.