Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An tsinci gawarwakin bakin hauren Somaliya su 20


Dubban 'yan gudun hijiran Somaliya
Dubban 'yan gudun hijiran Somaliya

‘Yan sanda a Tanzaniya sun ce wasu bakin hauren Somaliya su 20 sun

‘Yan sanda a Tanzaniya sun ce wasu bakin hauren Somaliya su 20 sun shake har lahira a yayin yinkurin fasa kwabrinsu ta cikin kasar.

Su ka ce an tsinci gawarwakin maza 17 da mata 3 a gefen hanya a yankin Morogoro da ke kasar ta Tanzania tsakanin ran 26 ga watan Disamba da kuma ranar zagayowar sabuwar shekara.

‘Yan sanda sun ce da alamar dai ‘yan fasa kwabrin mutane sun rinka jefar da gawarwakin bakin hauren ne daya bayan daya bayan sun mutu sanadiyyar rashin iskar shaka a yayin da ake jigilarsu cikin babbar mota zuwa Tanzaniya.

Somaliya dai na kara zama wata kasar da bakin hauren Somaliya ke bi zuwa Afirka ta Kudu. Dubban Somaliya ne ke tserewa daga kasarsu a kowane wata, a kokarinsu na kauce wa yanayin fari da kuma dadadden yaki.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG