Shugabar kasar Liberia Ellen Jonhson Sirleaf ta fara wa'adin mulki na biyu tare da yin alkawarin tabbatar da zaman lafiya da samar da aiyukan yi a kasar.
Litinin shugaba Sirleaf tayi wannan furuci, bayan an rantsar da ita a Monrovia baban birnin kasar. Sakatariyar harkoki wajen Amirka Hillary Clinton da wasu manyan jami'an gwamnati da kuma shugabanin kasashen Guinea da Benin da Senegal da Saliyo da kuma Ivory Coast ne suka halarci bikin rantsar da shugaba Sirleaf.
Wakilin Muryar Amirka Scott Stearns ya aiko da rahoton cewa shugabani masu hamaiya suma sun halarci bikin rantsar da shugabar, duk da zarge zargen da suka yi tunda farko cewa, shugaba Sirleaf ta lashe zaben ne ta hanyar magudi. Yace tunda farko masu hamaiya sun bukaci ayi zanga zanga a ranar litinin, amma kuma daga baya suka soke wannan bukata domin a samu zaman lafiya.
A yayinda take zantawa da yan jarida, sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ta yabawa yadda mulkin democradiya ta samu ci gaba a Liberia, amma kuma tayi kira ga shugaba Sirleaf ta yaki cin hanci da rashawa a wata ganawar da tayi da shugabar a kebe.
Ita dai kasar Liberia tana farfadowa daga yakin basasa da rikicin shekaru goma sha hudu da aka bbayansu a shekara ta dubu biyu da uku. A shekara ta dubu biyu da biyar shugaba Sirleaf ta zama mace Afrika ta farko da aka zaba bisa tafarkin mulkin democradiya. A bara ta zama daya daga cikin mata uku, wadanda aka baiwa lambar yabon samun zaman lafiya ta Nobel.