Kwamitin sulhu na MDD yana kira ga kasar Guniea Bissau ta kadamar da Zabe kan lokaci kuma cikin lumana, bayan mutuwar shugaban kasar, Mallam Bacai Sanha farkon makon nan.
Kwamitin mai wakilai 15 yace tilas sojoji su mutunta tsarin mulkin farar hula, daga nan kwamitin ya bukaci hukumomin kasar su dauki karin matakan tsaro domin hana barkewar tarzoma.
Rundunar mayakan kasar tana cikin shirin ko-ta-kwana, inda aka sauke tutocin kasar kasa, a lokcin zaman makoki na mako daya wadda zai biyo bayan jana’izar Mr. Sanha ranar lahadi.
Ya rasu ne ranar lahadi a wani asibiti a birnin Paris, bayan ya juma yana fama da cutar da ba a bayyana ba. Ya mutu yana da shekaru 64 a duniya.