Wani kakakin mayakan Kenya ya bada labarin dakarun kasar sun kai farmaki da jiragen yaki kan mayakan sakai dake da nasaba da al-Qaida a kudancin Somalia, a wani bangaren shirin kokarin tusa keyarsu daga kasar.
Kakakin, kanal Cyrus Oguna, ya gayawa manema labarai yau Asabar cewa an kashe akalla mayakan sakan al-shabab 60 a farmkain da suka kai jiya jumma’a a garin Grabaharey a yankin Gedo na Somalia. Yace an tseguntawa musu inda mayakan suke kamin su kai farmakin, kuma yana jin adadin wadan da suka halaka sakamkon harin zai karu.
Mayakan Kenya sun kutsa cikin Somalia a watan oktoba domin su fatattaki ‘yan kungiyar ta al-shabab, wacce take iko kan sassar kasar mai yawa, wacce Kenyan take zargi da laifin shiga kasarta ta saci mutane.