Dubun dubatan mutane sun taru a jiya Lahadi a dandalin wasannin motsa jigi na rugby da ke birnin Bloemfontein da ke Afirka ta Kudu don murnar cikar shekaru 100 na jam’iyyar African National Congress (ANC) mai mulki.
Wannan gawurtaccen shagali, wanda ya hada da jawabi daga shugaban ANC kuma shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma, za a kammala shi ne da wasu jerin bukukuwa a karshen mako na murnar zagayowar ranar kafa jam’iyyar da ta fi dadewa a nahiyar Afirka.
Tunda da farko da tsakaddaren, Shugaban kasar Afirka ta Kudu ya kunna fitilar murnar cika shekaru 100 a majami’ar Bloemfontein inda ‘yan gwagwarmayar bakaken fata da masu iliminsu su ka kafa jam’iyyar a ran 8 ga Fabrairun 1912.
Dinbin shugabanni daga sauran kasashen Afirka sun bi sahu don karrama jam’iyyar ANC, wadda Nelson Mandela ya jagoranta zuwa gadon mulki bayan faduwar manufofin banbancin launin fata.
Mr. Mandela dai bai sami zuwa bikin ba saboda dada tagayyara da ya yi.
An kafa ANC ne saboda bukata da kuma aniyar yakar dabi’ar nuna bambancin launin fata, kuma gwagwarmayar da ta yi ya kai ga karshen mulkin tsirarun fararen fatan Afirka ta kudu a 1994.
Nelson Mandela ya zama bakar fata na farko da ya shugabanci wannan kasar.