Jami’an tsaro a Bahrain sun yi ta harbe-harben gargadi a lokacin da jama’ar das u ka taso daga wurin jana’iza su ka yi kokarin komawa Babban Dandalin birnin Manama wanda hakan nuna turjiya ne ga haramta zanga-zanga da gwamnati ta yi. Wani asibiti y ace an kawo dinbin wadanda su ka sami raunuka a yamutsin na yammacin Jumma’a.
Wani wakilin Muryar Amurka mai suna Philip Wellman y ace ya ga mutane da dama da abin ya rutsa das u a asibiti. Jama’a da dama sun taru a harabar asibitin cikin fishi, da yawansu na ta daga murya da cewa “Allah wadaran Khalifa.” Wato Sarkin Bahrain Hamad bin Isa al-Khalifa.
Tun kuma da safiyar yau Jumma’a a wurin jana’izar wasu da abin ya rutsa da su, masu jana’izar, wadanda galibinsu ‘yan Shi’a ne sun yi ta ambaton kalaman neman a hambare gwamnatin da ‘yan Sunni ke wa jagoranci.
Babban Malamin Shi'a na kasar ya bayyana abka wa masu zanga-zangar da jami'an tsaro su ka yi da cewa murkusa jama'a ne. A yayin sallar Jumma'a a wani kauyen da ke Arewa maso yammacin kasar, Sheikh Isa Qassem ya ce gwamnati ta rufe kofofin shawartawa.
Daruruwan magoya bayan gwamnati masu kada tutocin kasar ma sun yi ta zanga-zanga a yau Jumma'a a babban birnin kasar