Amurkawa na shagulgulan Hutun Karrama Shugabannin kasar a yau Litini, inda su ke girmama biyu daga cikin shugabannin kasar da su ka fi fice.
An kirkiro hutun ne a 1968, inda aka ware ranar Litini ta uku a watan Fabrairu don shagulgulan ranar haihuwan shugaban Amurka na farko George Washington.
Shugaban Amurka na 16, Abraham Lincoln, shi ma a watan Fabrairu ne aka haife shi, kuma Amurka na daukar wannan ranar ta girmama musamman wadannan shugabannin biyu ne.
Miliyoyin Amurkawa basu zuwa aiki a wannan ranar a sailinda ofisoshin gwamnati da dama da makarantu ke rufe.
An jima ana tunawa da ranar 22 ga watan Fabrairu da aka haihuwar Washington kafin ta zamo ranar hutu ta kasa baki daya. A cikin 1885 ne aka fara tunawa da ranar.
Haka zalika Amurkawa a jihohi da dama sun yi ta tunawa da ranar haihuwar Lincoln ta 12 ga watan Fabrairu bayan kashe shi nan da nan bayan yakin basasa a 1865.