Wata kotun daukaka karat a China ta tabbatar da hukuncin da aka zartas kan wani mai ilimin kimiyyar yanayin karkashin kasa wanda ake zargi da laifin tara bayanai game da bangaren main a China.
Kotun ta Beijing a yau Jumma’a ta ki amincewa da daukaka karar da Xue Feng ya yi kan hukuncinsa na daurin shekaru 8 da wata kotu ta zartas masa a watan Yulin day a gabata. Xue wanda ba-Amerike ne dan asalin China, an kama shi ne a watan Nuwamban 2007 bayan ya yi yinkurin sayar da bayanai kan bangaren mai na China. Xue dai na aiki ne a wani kamfanin makamashi da kuma kwararru kan harkar mai mallakin wasu Amurkawa a lokacin da aka kama shi.
Lauyan Xue y ace a baya bayanan da ake takaddama akansu na nan a kasuwa, an maida su wasu abubuwan sirri ne bayan da Xue ya same su.
Jakadan Amurka a China Jon Huntsman ya halarci zaman kotun nay au Jumma’a. Ya gaya wa manema labarai a harabar kotun cewa ya yi takaici sosai da hukuncin, to amman y ace dama abu ne mai yiwuwa
Huntsman ya yi kira ga gwamnatin China ta saki Xue ba tare da bata lokaci ba bisa dalilin tausayi.