Shaidu a kasar Bahrain sun ce dubban masu zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati su na kwarara zuwa dandalin nan da ake kira "Dandalin Lu'ulu'u" a Manama, babban birnin kasar, a bayan da 'yan sanda suka janye daga wannan wuri.
Kafofin labarai sun ce tunda fari, a yau asabar, 'yan sandan sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa 'yan zanga-zangar a bayan da sojoji suka janye tankokinsu daga wannan dandali.
Babbar kungiyar hamayya ta ‘yan mazhabin Shi’a a Bahrain, ta ce tilas ne gwamnatin kasar ta yi murabus, a kuma janye sojoji daga kan tituna, yayin da zanga-zangar siyasa take ci gaba da yaduwa kamar wutar daji a fadin gabas ta tsakiya da Arewacin Afirka. Kungiyar Wefaq, wadda ta janye daga cikin majalisar dokoki a wannan makon, ita ce ta mika wannan bukata yau asabar a bayan da masarautar kasar Bahrain ta yi tayin gudanar da tattaunawa ta kasa baki daya domin kawo karshen wannan zanga-zanga.
A kasar Libya, kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch ta ce a bisa rahotannin da aka samu daga ma’aikatan asibiti da kuma shaidu, an kashe mutane akalla 84 a farmakin da aka kai kan masu zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati. Kungiyar ta ce a jiya jumma’a, dakarun tsaro sun kashe ‘yan zanga-zanga su akalla 35 a birnin Benghazi.
A kasar Yemen kuma, an kashe akalla mutum guda, yayin da 28 suka ji rauni a bayan da wani mutumi a cikin mota ya jefa gurneti a kan masu zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati a birnin Taiz dake kudu maso yammacin kasar. An kai farmaki a daidai lokacin da ‘yan zanga-zanga suke gudanar da gangamin ranar nuna fusata a birane da garuruwan kasar. Wasu shaidu sun dora laifin wannan hari a kan gwamnati.
A kasar Jordan kuma, ‘yan zanga-zanga sun bai wa hammata iska a lokacin da aka yi arangama a tsakanin magoya bayan gwamnati da masu zanga-zangar neman sauyin siyasa. Akwai rahotannin dake cewa mutane akalla 8 sun ji rauni a lokacin da magoya bayan gwamnati dauke da kulakai suka far ma ‘yan zanga-zangar.
A kasar Iran, dubban ‘yan zanga-zanga masu goyon bayan gwamnati, sun yi kiran da a tsire shugabannin hamayya Mir Hossein Moussavi da Mehdi Karroubi. An yi wannan kiran jim kadan kafin wani karamin gangami na masu goyon bayan gwamnati. ‘Yan hamayya sun yi kira ta hanyar sadarwar Internet da a yi gangami gobe lahadi a fadin kasar domin nuna goyon baya ga Moussavi da Karroubi tare da jimamin mutane biyu da suka mutu a lokacin zanga zangar nuan kin jinin gwamnati wannan makon.
A Algiers, babban birnin Aljeriya kuma, ‘yan kasar su na hallara domin gangamin neman saukar shugaba Abdelaziz Bouteflika daga kan mulki. An haramta gudanar da wannan zanga-zanga an kuma dauki tsauraran matakan tsaro a wurin da aka shirya yinta, inda aka ce ‘yan sanda cikin damara su na kokarin karkasa ‘yan zanga-zangar zuwa gungu-gungun da ba su da yawa. An gudanar da irin wannan gangami a makon jiya, koda yake ‘yan sanda sun hana ‘yan zanga-zangar masu yawa isa wurin da aka shirya gudanarwa.