Jiya Alhamis sojoji a Bahrain sun karbi iko a babban birnin kasar,bayanda ‘yan Sanda suka yi amfani da albarusan roba,da borkono mai sa hawaye yayinda suka kai somame kan sansanin masu zanga zanga,suka kashe mutane biyar,suka jikkata230.
Tankoki da motoci masu sulke sun mirgina cikin Manama,sojoji suka girke wurare binciken motoci. Sojoji cikin damara suna sintiri kan titunann birnin.Ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta gargadi ‘yan kasar ta sakon Text cewa su zauna gida.Bankuna da wasu cibiyoyi basu yi aiki ba.
Ministan harkokin wajen kasar,Sheikh Khalid bin Ahmed Khalifa,ya kare fatattakar da gwamnati ta yi wa masu zanga zanga domin acewarsa masu zanga zanga da suka cika dandalin Pearl da galibinsu ‘yan shi’a ne suna raba kawuna suna neman kai kasar ga fitina ta sabanin akida.Rundunar mayakan kasar ta haramta duk wani irin taro a bainar jama’a.
Ministan harkokin kiwon lafiyar kasar yace an kashe mutane uku a kokarin tarwatsa masu zanga zanga a dandalin Pearl.Amma likitoci suka ce akalla wasu mutane biyu sun rasu,da kuma da dama da suka jikkata wasu da raunuka masu tsanani.Akwai rahotanni dake cewa akwai ‘yanzanga zanga da dama da ba’a san inda suke ba.
Wakilan majalisar dokoki karkashin jam’iyyar alWefaq ta ‘yan shi’a jam’iyyar hamayya mafi girma a Bahrain sun yi murabus baki dayansu bayan arangamar ta jiya Alhamis. Wakilan jam’iyyar su 18 cikin majalisar mai kujeru 40 sun sha alawashin ba zasu dawo ba sai sarki Hamad bin Isa al-Khalifa ya amince da sake tsarin kasar kan tafarkin mulki masarauta mai tsarin mulki da za’a zabi wakilanta. Ahalin yanzu kuma,Amurka ta yi kira ga Bahrain kada ta yi amfani da karfi kan masu zanga zanga cikin lumana. Kakakin fadar White House,Jay Carney yace shugaba Obama ya yi ta’aziyya ga iyalan wadanda tarzomar ta rusa da su a arangama da ‘yansanda jiya Alhamis.