Alassane Quattara, daya daga cikin shugabannin kasar Ivory Coast biyu dake hamayya da juna, yace yunkuri na baya bayan nan na warware rudamin siyasar kasar shine “matakin karshe”.
Mr. Quatarra ya gana da shugabannin kasashen nahiyar Afrika guda hudu jiya Talata a Abidjan babban birnin kasar Ivory Coast, wadanda Tarayyar Afirka ta dorawa alhakin warware rikicin.
Shugaban kasar mai ci yanzu Laurent Gbagbo ya yi watsi da matsin lambar da ake yi mashi na neman ya mika mulki ga Mr. Quattara, wanda Majalisar Dinkin Duniya ta hakikanta cewa shine ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Nuwamba.
Mr. Quatarra ya shaidawa tawagar cewa, masu shiga tsakani na baya sun shaidawa Mr. Gbagbo karara cewa ya fadi zabe kuma tilas ya mika mulki cikin ruwan sanyi. Ya kuma bayyana takaicin ganin haka bata yiwu ba.
Ranar Litinin shugabannin Tarayyar Afirka suka gana da Mr. Gbagbo. Daya daga cikin shugabannin dake tawagar shiga tsakanin ya fice daga tattaunawar bayanda kungiyar mayaka dake goyon bayan Mr. Gbagbo suka yi barazanar kashe shi.
Shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore ya soke tafiyarshi zuwa Ivory Coast ranar Litinin. Mr. Gbagbo yana zargin shugaba Compaore da goyon bayan Mr. Quatarra.