A shalkawatar EFCC, Mukaddashin shugaban hukumar Ibrahim Magu ya bayyana cewa ko a jiya Talata saura kadan su damke wani barawon biro na Najeriya, kuma duk da haka suna nan suna aiki tukuru domin kunyata masu yiwa arzikin kasar zagon kasa.
Wannan ya biyo bayan lokacin da kungiya mai da’awar yaki da zarmiya tazo gangamin matsawa gwamnatin shugaba Buhari ta binciki zargin almundahana tsakanin ministoci da sauran cibiyoyin gwamnatin kasar. Magu ya bukaci ya bukaci kungiyoyi masu zaman kansu su shiga tsarin fallasa asirin barayin biro dan a gurfanar da su gaban kuliya.
Magu, ya bayyana cewa ba gudu ba ja da baya wajan kamawa da gurfanar da duk wanda hukumar ta kama da laifin yin sama da fadi akan dukiyar al’umma, don haka ya bukaci taimakon al’umma da kungiyoyi masu zaman kansu domin fallasa duk wadanda ake zargi da satar kudin gwamnati.
Tun farko shugaban kungiyar Ibrahim Garba Wala, ya yi zargin jami’an gwamnatin Najeriya, na yiwa gwamnatin kasar zagon kasa ta hanyar sace dukiyar Baitul mali, kuma ya kara da cewa akwai akwai ma’aikatu da dama dake tafka al’mundahana. Daga karshe ya ce indai yakin da gwamantin Buhari ke yi dasu na gaskiya ne, to akwai bukatar a gaggauta daukar mataki a kansu.
Mata ma ba a barsu a baya ba wajan tofa albarkacin bakinsu yayin da ake gudanar da gangamin. Daga bisani kungiyar ta yi yunkurin shiga fadar shugaban Najeriya, domin mika wasika ga shugaba Buhari, amma jami’an ‘yan sanda suka hana.
Domin karin bayani saurari rahoton Nasiru Adamu El-hikaya.
Facebook Forum