Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Makafi Sun Yi Zanga-Zangar Lumana


Aliyu Bello Tola, Kwamishinan Kula Da Mata, Yara Da Kyautata Jin Dadin Jama'a Na Jihar Adamawa.
Aliyu Bello Tola, Kwamishinan Kula Da Mata, Yara Da Kyautata Jin Dadin Jama'a Na Jihar Adamawa.

Akalla daliban makarantar yara masu bukata ta musamman ta Jada dake jihar Adamawa, uku ke asarar rayukansu a duk zangon karatu wajen tsallaka titin Jada, zuwa Kojoli, domin neman ruwan sha.

Wannan bayani na kunshe cikin takardar koke da shugaban kungiyar makafi ta Najeriya, reshen jihar Adamawa, Komred John Tizhe Kwada, ya gabatarwa kwamishinan ma’aikatar kula da mata yara da kyautata jin dadin jama’a, sa’ilin wata zangazangar lumana mafi girma da ta kunshi mambobin kungiyar daga kananan hukumomi ashirin da daya.

Kungiyar ta kaddamar da zanga-zanga kan abin ta da kira maida su saniyar ware da gwamnatin Sanata Mohammadu Jibirila, ke nuna wa tun da ta amshi madafun mulki wajen aiwatar da ayyukan da suka shafi rayuwar mutane masu bukata ta msamman, ciki harda rabon mukamai na siyasa da kuma watsi da cibiyoyin koyar da sana’o’i na makafi.

Shima da yake zayyana bukatun kungiyar, sakataren kungiyar makafi ta Najeriya, reshen jihar Adamawa, Komred Christopher Livingstone, ya ce akwai ‘ya’yan kungiyar da suka sauke karatu a Manyan kwalejoji da jami’o’in da ke Najeriya, amma babu ayyukan yi, lamarin da ya sa daliban makarantar yara masu bukata ta musamman ke ta barace barace sakamakon kasawar hukumomi na ciyar da su.

Wadannan bututuwan ne wakilin sashin Hausa ya nemi dalibai da hukumomin makarantar su ba da Karin haske akai amma suka ce suna gudun gamuwa da fushin hukumar kula da ilimi mataki na farko ta jiha. Sai dai jin tabakin shugaban hukumar kula da ilimi mataki na farko na jihar Adamawa Alh. Hassan Mohammed Tola ya cutura.

A daya bangaren kuwa, kwamishinan ma’aikatar lura da mata, yara da kyautata jin dadin jama’a na jihar Adamawa Alh. Aliyu Bello Tola hakuri, ya baiwa kungiyar makafi ta Najeriya, reshen jihar Adamawa tare da alkawarin cika masu burin su.

Saurari Karin bayanin rahoton Sanusi Adamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00

Facebook Forum

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG