Bayan shugaban kasar Togo Gnassingbe Eyadema ya gana da shugaban Najeriya cikin sirri ya yiwa manema labarai karin bayani inda ya bayyana abun da ya kawoshi Najeriya.
Shugaban Togon ya ce ya zo Najeriya ne domin ya gana da shugaba Buhari ya kuma gode masa kan yadda ya taimaka a zaben sa a matsayin shugaban ECOWAS tare da nuna farin cikinsa bisa lafiyar da shugaba Buhari ya samu yanzu.
A cewar Shugaba Eyadema ya tattauna da shugaban Najeriya akan batutuwan da suka shafi kasashen yammacin Afirka. Kazalika sun duba batu matsalar tsaro a kasashen Liberia, da Guinea Bissau da kuma Togo.
Ta bakin tsohon jakadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya Ambassador Suleiman Dahiru, babu abun da Najeriya ba zata iya yi ba game da bada taimako. Yana cewa duk abun da shugaban Togo yake son Najeriya tayi, zata yi domin ta fi karfin bukatarsa. Yace duk abubuwan dake faruwa a kasashen ECOWAS Najeriya zata iya shiga tayi abun da ya kamata. Ya bada misali da rigingimun Liberia da Saliyau inda Najeriya ta kashe miliyoyin daloli tare da hasarar sojojinta.
Shugaban Togon ya himmatu akan yadda ECOWAS ta rage kwamishinonin ta daga 15 zuwa 9 lamarin da tsohon sakataren raya kogin Kwara mai kasashe tara, Alhaji Bababo Abba, ya ce yayi daidai kuma bai zo da mamaki ba saboda kowace kasa akwai kudin da ya kamata ta biya a shekara amma yawancinsu ba sa biya.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani
Facebook Forum