Tun a watan Yulin daya gabata ne majalisar dokokin Najeriya, ta kammala mahawara tare da amincewa a gudanar da sauye sauyen da zai shafi batutuwa guda 33 a cikin kundin tsarin mulkin kasar.
Mafiya daukar hankali daga cikin wadannan batutuwa sune, baiwa kananan hukumomi da majalisun dokoki na jihohi ‘yancin kai ta fuskar kudi, da samar da dangantakarar Indipenda da sauran su.
Yanzu haka wasu daga cikin ‘yan majalisar dokokin jihar Jigawa sun fara bayyana ra’ayin su game da wasu daga cikin wadannan batutuwa gabanin gabatar da kudirin ga zauren majalisar. Hon Ahmed Garba shine mataimakin shugaban majalisar.
Kungiyoyin sa kai dana gwagwamaryar inganta demokaradiyya sun dade suna kamfe domin ganin an raba asusun hadaka tsakanin gwamnoni da majalisun kananan hukumomi, baiwa majalisa ‘yanci da kuma samar da gurbin dan takarar indipenda a kundin tsarin mulki, kamar yadda Comrade Kabiru Sa’idu Dakata na kungiyar CITAD a Kano ya bayyana.
A shekarun baya wannan yunkuri ya ci karo da cikas a matakin majalisun dokoki na jihohi, amma masu kula da al’amura sun dora alhakin hakan akan gwamnoni.
Daga Kano ga rahotan Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko mana.
Facebook Forum