A wani taron limaman Katolika na rundunar sojojin na shekarar 2018 da aka yi a Birnin Maiduguri dake jihar Borno, Janar Tukur Buratai, ya bayyana yadda sojoji ke kakkabe ‘yan Boko Haram a kauyukan jihar.
Kwamandan Operation Lafiya Dole dake Birnin Maiduguri, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, shine ya wakilci Janaral Buratai wajen wanan taro. Ya ce rikicin kungiyar Boko Haram ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da ma raunata tattalin arziki. Amma yanzu haka suna dap da kawo karshen ‘yan ta’addan.
Inji kwamandan sojojin suna aiki tukuru, musamman a kauyuka domin kawo karshen ta’addancin. Misali, a arewa maso gabashin Najeriya rundunar hadin gwuiwa na kasa da kasa da Operation Lafiya Dole sun maido da zaman lafiya a garuruwan da a baya suna karkashin kungiyar Boko Haram. Ya kara da cewa suna kokarin kakkabe sauran ‘ya’yan Boko Haram dake cikin dajin Sambisa.
Babban limamin Katolika na rundunar sojojin Najeriya, Birgediya Charles Tidi cewa ya yi sojojinsu dake jihar suna kokari, idan ba domin sun sadakar da kansu ba, da lamarin ba haka yake ba a wannan yankin. Ya ce saboda haka ne suka zo su jinjinawa sojojin, su yaba masu da kuma yi masu addu’a.
Bishop Naga Muhammad William shugaban kungiyar CAN reshen jihar Borno wanda ya halarci taron yana mai cewa annobar ta shafi kowa da kowa saboda haka a yi addu’a tare da goyon bayan sojojin, Allah ya kawar da ita. Ya ce yanzu ana samun walwala ba kamar da ba, kuma yana fatan ta dore. Ya yi kira a hada kai domin a kawo karshen tashin tashinar.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani
Facebook Forum