Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawan Mamata Na Karuwa A Mubi


Ya zuwa yanzu alkalumman wadanda suka rasa ransu a wani harin kunar bakin wake da wani yaro ya kai a wani Massalaci yayin sallar asuba a garin Mubi dake jihar Adamawa na karuwa.

Wannan ya biyo bayan tashin wani bom a yankin Madagali da kuma kissan gillar da aka yiwa wasu matan Filani makiyaya da ‘ya’yansu fiye da talatin a yankin Numan,dake kudancin jihar Adamawa, lamarin da yanzu haka ya sa aka tura jami’an tsaro don neman masu hannu a kissan gillar.

Kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar ta Adamawa, SP. Othman Abubakar, wanda ya bayyana halin da ake ciki game da harin kunar bakin waken da kuma kissan da aka yiwa Fulanin, da kuma matakan da aka dauka a yanzu, ya ce rundunar ta sha alwashin kiyaye dukiyoyi da rayukan jama’a.

Ya kara da cewa kasancewar jami’an tsaro a yankin zai taimaka gaya wajen tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da tsaro a yankin na Madagali.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:43 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG