Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Harin Jirgi Mara Matuki Ya Fada Kan Wani Birnin Isra’ila


Firai Ministan Isra'ila, Netanyahu, hagu yayin wani taron manema labarai a Tel Aviv
Firai Ministan Isra'ila, Netanyahu, hagu yayin wani taron manema labarai a Tel Aviv

Baya ga harin jirgi mara matukin na ranar Alhamis, an kakkabo sauran makaman ko kuma sun rikito da kansu a cewar Reuters.

Wani jirgi mara matuki ya fada akan wani ginin fararen hula a birnin Eilat da ke kudancin Isra’ila a ranar Alhamis.

Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito dakarun Isra’ilan suna cewa harin ya yi ‘yar barna.

Mayakan Houthi na Yemen sun ce sun harba wani makami mai linzami a yankin birnin da ke bakin Teku.

Mayakan Houthi mai alaka da Iran ta sha kai hare-haren makamai masu linzami da jirage mara matuka akan Isra’ila tun bayan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba akan Isra’ila da kuma rikicin da ya biyo baya.

Baya ga harin jirgi mara matukin na ranar Alhamis, an kakkabo sauran makaman ko kuma sun rikito da kansu a cewar Reuters.

Dakarun kasar sun ce suna ci gaba da gudanar da bincike kan jirgin mara matukin da ya fada kan ginin na birnin Eilat, amma ba su fadada bayanansu ba.

Babu dai wanda ya jikkata a harin.

A ranar ta Alhamis, dakarun na Isra’ila sun ce makaman kariyarsu sun datse wani harin makami mai linzami da aka harbawa Isra’ila a kusa da Teku, sannan makaman kariya har ila yau sun datse wani hari na daban a kudancin Negev da ke hamada.

Mayakan Houthi sun ce sun harba jerin makamai masu linzami da suka kaikaici Isra’ila ciki har da wani wuri da kakakin kungiyar ya kwatanta a matsayin sansanin soji.

Su dai dakarun Isra’ila ba su dora alhakin harin na makami mai linzami akan kowa ba ko kuma wadanda aka datse a yankin Negev.

Houthi na daga cikin kawancen da Iran ta kafa da ya hada har da kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon da ke goyon bayan Hamas.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG