Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hezbollah Ta Harba Rokoki Sama Da 200 Cikin Isra'ila


Israeli-Hezbollah (Photo by Kawnat HAJU / AFP)
Israeli-Hezbollah (Photo by Kawnat HAJU / AFP)

Kungiyar Hezbollah ta kasar Labanon ta ce ta harba rokoki sama da 200 ne a wasu sansanonin soji da ke Isra'ila a matsayin ramuwar gayya kan harin da ya kashe daya daga cikin manyan kwamandojinta.

Harin da kungiyar, da Iran ke marawa baya, ta kai a ranar Alhamis na daya daga cikin mafi girma a rikicin da aka kwashe watanni ana gwabzawa a kan iyakar Lebanon da Isra'ila.

Sojojin Isra'ila sun ce an harbo "makamai masu linzami da kuma wasu munanan hare-hare ta sama" kasarsu daga Lebanon, wadanda aka tare yawancinsu.

Kawo yanzu dai babu rahoton asarar rayuka.

A ranar Laraba ne Isra’ila ta dauki nauyin kashe Mohammad Naameh Nasser, jagoran daya daga cikin sassan yankuna uku na Hezbollah a kudancin Lebanon, a ranar Talata.

Lebanon ta harba rokoki kan Isra'ila
Lebanon ta harba rokoki kan Isra'ila

Sa'o'i kadan bayan haka, kungiyar Hezbollah ta harba rokoki da dama cikin arewacin Isra'ila da kuma yankin Golan Heights na Siriya da ta mamaye. Ta harba wasu rokoki a ranar Alhamis din nan, ta kuma ce ta aika da jiragen sama marasa matuka masu fashewa.

Amurka da Faransa na ci gaba da yin kame-kame don hana fadan da ake gwabzawa, wanda suke fargabar zai iya mamaye yankin.

Rikicin dai mai karamin karfi ya fara ne jim kadan bayan barkewar yakin a Gaza. Hezbollah ta ce tana kai wa Isra'ila hari ne domin nuna goyon bayanta ga Hamas.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG