Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Hezbollah Ta Sha Alwashin Hukunta Isra’ila Kan Mummunar Fashewar Na’urorin Sadarwa

ISRAEL-PALESTINAINS/HEZBOLLAH-GOLD APOLLO
ISRAEL-PALESTINAINS/HEZBOLLAH-GOLD APOLLO

A yau Laraba, a sanarwar da ta wallafa a shafinta na Telegram, kungiyar Hezbollah ta sha alwashin ci gaba da gwagwarmayar tallafawa al’ummar Gaza sannan ta yi alkawarin daukar fansa a kan harin na jiya Talata.

Kungiyar Hezbollah ta sha alwashin daukar fansa akan isra’ila sakamakon mummunar fashewar daruruwan na’urorin sadarwar da mayakanta ke amfani dasu a lokaci guda a fadin kasar Lebanon.

A yau Laraba, a sanarwar da ta wallafa a shafinta na Telegram, kungiyar Hezbollah ta sha alwashin ci gaba da gwagwarmayar tallafawa al’ummar Gaza sannan ta yi alkawarin daukar fansa a kan harin na jiya Talata.

Jerin fashe-fashen sun kashe mutane 9, ciki har da wata yarinya, tare da raunata wasu mutum 2, 800. 200 daga cikinsu na cikin mawuyacin hali, a cewar Ministan Lafiyar Lebanon Firass Abiad a jiya talata.

Har yanzu Isra’ila ba ta ce uffan ba akan fashe-fashen ba.

Sa’o’i da dama gabanin harin, Isra’ila ta sanar da cewa tana fadada yakin da harin kungiyar Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba ya haddasa.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG