Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

“Dole Isra'ila Ta Kara Kaimi Wajen Bari Ana Ayyukan Jinkai A Gaza" - Blinken


SAUDI-US
SAUDI-US

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya fada jiya Litinin cewa, dole ne Isra’ila ta kara kaimi wajen bada damar kai agajin jinkai a zirin Gaza da aka yi wa kawanya.

WASHIN GTON, D. C. -Blinken ya kuma ce zai yi amfani da ziyararsa ta Gabas Ta Tsakiya, wacce ta ke ziyararsa ta bakwai a yankin tun bayan barkewar yakin na Isra’ila da Hamas a watan Oktoba, wajen tattauna wannan batu tare da shugabannin Isra'ila.

Da yake magana a wani taron da aka yi a (Riyadh) babban birnin Saudiyya, Blinken ya ce hanya mafi dacewa ta sassauta bala'in jinkai a Gaza ita ce kulla wata yarjejeniyar tsagaita wuta da ba za a iya kawar da ita ba, wadda kuma za ta sako mutanen Isra'ila da Hamas ta yi garkuwa da su tun bayan harin da ta kai a ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

Antony Blinken - Egypt, Jordan, Saudi Arabia, Qatar, the United Arab Emirates, Palestinian Authority - Four Seasons Hotel Riyadh, Afrilu 29, 2024.
Antony Blinken - Egypt, Jordan, Saudi Arabia, Qatar, the United Arab Emirates, Palestinian Authority - Four Seasons Hotel Riyadh, Afrilu 29, 2024.

Isra'ila ta yi wa Hamas tayi "mai cike da kyautatawa" da ya ke fatan kungiyar za ta karba, in ji shi.

"An yi matukar kyautatawa a bangaren Isira'ila, kuma a halin yanzu, Hamas ce shamaki tsakanin al'ummar Gaza da tsagaita wuta," in ji shi a wani taron tattalin arzikin duniya a Riyadh.

"Dole ne su yanke shawara, kuma dole ne su yanke shawarar da sauri. Don haka, muna neman tabbaci, kuma ina fatan za su yanke shawarar da ta dace kuma za mu iya samun canji mai mahimmanci a wannan al'amarin, "in ji Blinken.

Ko da yake ana ci gaba da tattaunawa, kawo yanzu Hamas ta yi watsi da wasu tayin da Masar, Qatar da Amurka suka yi, kuma Isra'ila ta amince da su. Ko ba a cimma wata yarjejeniya ba, Blinken ya ce yana da matukar muhimmanci a inganta halin da ake ciki a Gaza yanzu.

"Har ila yau, ba ma jira a tsagaita wuta kafin daukar matakan da suka dace don biyan bukatun fararen hula a Gaza," a cewar Blinken ga ministocin harkokin wajen kasashen yankin Gulf da safiyar ranar Litinin, lokacin da ya isa Saudi Arabiya don fara ziyararsa ta kasashen Gabas Ta Tsakiya. Ziyarar za ta hada da zuwa Jordan da Isra'ila a ranakun Talata da Laraba.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG