Gwamnatin Koriya ta Arewa na gargadin Koriya ta Kudu da sauran kasashen duniya da su san cewa ba wani chanji da za’a samu a mmanufofin Koriya Ta Arewa din a karkashin mulkin sabon shugabanta, Kim Jong Un. Kwana daya bayanda aka kamalla zaman makokinrashin tsohon shugaban kasar Kim Jong Il ne, majalisar tsaro ta KTA ta aika wannan sakon jan kunnen ga abinda ta klira “sakarkarun ‘yan siyasa na duniya” inda take cewa:
A cikin natsuwa da karfin zuciya, muna sanarda shashashun ‘yan siyasa duniya, ciki har da gwamnatin jeka-nayi-ka ta Koriya ta Kudu, cewa kada su sa ran ganin wani chanji daga wurinmu.”
Sanarwar taci gaba da cewa KTA ba zata taba wata harka da shugaban Koriya Ta Kudu Lee Myung-bak ba, ta kuma ce al’ummar Koriyan Ta Aarewa zasu bada cikakken goyon bayansu ga sabon shugabansu Kim Jong Un.