Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan Ruwan Amurka Sun Kubutar da 'Yan Iran Daga Hanun 'Yan Fashi


Jirgin Yakin Ruwa na Amurka USS Kidd da ya kaiwa jirgin masuntan Iran doki.
Jirgin Yakin Ruwa na Amurka USS Kidd da ya kaiwa jirgin masuntan Iran doki.

Wani jirgin ruwan mayakan Amurka ya kubutar da ‘yan kasar Iran 13 da mafasa cikin ruwa suke garkuwa dasu a tekun Arabia.

Wani jirgin ruwan mayakan Amurka ya kubutar da ‘yan kasar Iran 13 da mafasa cikin ruwa suke garkuwa dasu a tekun Arabia, kwanaki bayan da Farisar da gargadi jiragen yakin Amurka kada su dawo ruwaye dake yankin Gulf.

A jiya jumma ce rundunar mayakan ruwan Amurka ta bada labarin ta tsare ‘yan fashi goma sha biyar, bayan da farisawan da suke garkuwa dasu suka yi kukan neman doki. Rundunar tace wata tawagar jami’anta daga jirgin yakin d a ake kira USS Kidd sun hau jirgin ruwan masuntan bayan d a suka lura da karamin jirgin ‘yan fashin yana makale da jirgin masuntan ‘yan kasar Iran.

Rundunar sojojin ruwan amurka tace ta hakikance ‘yan fashin suna garkuwa da mutanen fiyeda wata daya, kuma sun mai da jirgin helkwatar su. Rundnar tace ta hakikance cewa ‘yan fashin sun tilastawa wadan da suke garkuwa taimaka musu a fashin da suke yi.

Kakakin rundunar mayakan Amurka Rebecca Rebarich ta gayawa sashen Farsi na MA cewa rundunar mayakan maurka suna sane da cewa jirgin da suka kaiwa doki yana dauke da tutar irin, duka da haka tace wajibi ne jiragen ruwa suka kai doki ga duk wani dake cikin teku dake cikin mawuyacin hali ba atreda la’akari da kasar da suka fito ba.

Kanal Rebarich tace keftin na jirgin ruwan masuntan ya bayyana matuka rgodiya ga mayakan ruwan Amurkan, ya bayyana fargaban cewa in ba domin dokin d a Amurkan ta kai musu ba da za a shafe watanni mafasan asuna garkuwa da su.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG