Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Tana Kashedi Ga Kawayenta A OPEC


Tashar hakar mai
Tashar hakar mai

Wakilin Iran a kungiyar kasashe masu arzikin mai watau OPEC yana kashedi ga kasashen larabawa makwabta cewa kada su kuskura su kara yawan mai da suke hakowa idan har kasashen yamacin duniya suka kakaba mata takunkumin hana sayen mai

Wakilin Iran a kungiyar kasashe masu arzikin mai watau OPEC yana kashedi ga kasashen larabawa makwabta cewa kada su kuskura su kara yawan mai da suke hakowa idan har kasashen yamacin duniya suka kakaba mata takunkumin hana sayen mai daga kasar.

A wani rahoto da jaridar Sharq ta buga yau, ta ambaci Mohammed Ali khatibi, yana cewa Tehran zata fassara irin wan nan mataki a matsayin rashin mutunci. Haka kuma yace idan wasu kasashe dake OPEC suka yi haka to Allah kadai yasan abinda matakin zai haifar.

A makon jiya, jami’an difilomasiyya daga kasashe dake yammacin duniya suka bayyana damuwarsu kan shirin Iran na tsarkaka sinadaran Uranium zuwa wani daraja, suna cewa hakan ya saba kudurorin Majalisar Dinkin Duniya kan shirin nukiliyar Farisar da ya janyo gardama.

XS
SM
MD
LG