Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Illar Raba Dare Ana Waya/Chatting Ga Matasa Da Al'umma, Daga Dr Mai Kano


Shirin samartaka na karshen wannan makon ya sami bakucin malami a fannin zamantakewa da halayyar dan’adam daga jami’ar Bayero dake jahar Kano kuma yayi mana cikakken bayani akan illar da wayar hannu ke haifarwa ga al’umma da kuma matasa samari da ‘yan mata musamman wadanda ke raba dare suna hira ta wayar hannu, ya kuma bada shawarwari ga iyaye da matasa baki daya.

Wayar hannu nada matukar amfani a rayuwar dan’ adam da kuma al’uma kanta, sai dai a lokuta da dama kamar yadda babban bakon namu ya bayyana, akan sami wasu wadanda kan yi amfani da irin wannan damar domin yin wasu abubuwa da kan iya zama da illa ga rauywa.

Akwai samari da ‘yan mata da dama da kan shafe sa’oin da yakamata su kwanta domin ba jikunan su hutu suna waya musamman ciki dare. Wannan na da illa ga lafiyar su da kuma gurbata tarbiyya domin kuwa shafe dare bakidaya ana hira a irin wannan lokacin ke sa wasu maganganun batsa da sauransu su fara bullowa wanda daga karshe bata haifar da ɗ a mai ido.

Zaku iya saurarar cikakken shirin a shafin mu na Dandalinvoa.com a kowane lokaci, Dandalinvoa duniya a tafin hannun ku.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG