An kaddamar da aikin wayar da kan jama’a, game da allurar riga kafin cutar Bakon Dauro, a jihar Neja.
Cutar Bakon Dauron dai na daya daga cikin cututtukan da hukumar lafiya ta duniya, ke fatan ganin an kawar da ita masamman a kasashe masu tasowa.
Dr. Fati Abdalla, darakta, a sashen riga kafin cututtuka na ma’aikatar lafiyar jihar Neja, ta ce illar Bakon Dauro, ga yaron da baida riga kafi ba wai kurajen dake fitowa a jiki bane, ya kansa yaro ya rasa muryarsa, ido ko ya samu tabuwar kwakwalwa ko kuma mutuwa.
A jihar Neja, dai akwai tarar Naira 50.000, ko daurin shekaru 5, ga duk wanda ya ki bari a yiwa yaronsa riga kafi. Za dai a fara yin wannan riga kafi ne a jihar Neja daga ranar 21 zuwa 25, ga wannan watan da muke ciki.