Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasa Ta Rufe Wasu dake Hakar Ma'adanai a Jihar Neja


 Masu hakan ma'adanai suna fitowa daga rami
Masu hakan ma'adanai suna fitowa daga rami

Wasu da ake kyautata zaton suna hakan ma'adanai ba bisa kaida ba kasa ta rufe su har hudu sun halaka biyu kuma sun tsira da ransu

Mutane biyu ne suka mutu kana wasu biyu suka jikata lokacin da kasa ta rubta masu a wurin wani aikin hakan ma'adanan kasa a jihar Neja.

Lamarin ya faru ne a kauyen Shadadi dake cikin karamar hukumar Mariga. Aminu Ahmed Shadadi yana cikin masu sana'ar ma'adanan karkashin kasa a yankin kuma ya kara haske akan lamarin.

Yace abun ya faru ne lokacin da suke cikin ramin suna hako ma'adanai. Su shida ne suke ciki sai kasa ta rufesu cikin ramin da suke.

Malam Musa Yakubu Shadadi yace biyu daga cikin wadanda suka mutu 'yan uwansa ne. Inji shi Malam Yakubu kowa a cikin garin na cikin juyayi da alhini.

Amma daya daga cikin masu kamfanonin hakar ma'adanan karkashin kasa a jihar Neja Alhaji Danlami Sarkin Daji yace wadanda suke aikin ba kan kaida ba ne lamarin ya shafa.Yace akwai hadari tare da aikin amma su matasan shaye-shye suke yi su fada ramin suna neman hako ma'adanai.

Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta jihar ta bayyana damuwa akan lamarin. Tace tana fadakarwa akan illar dake tattare da aikin hakan ma'adanan kasa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG