Mahukunta ne suka fadi hakan, to sai dai har yanzu b’ a gane ainihin dalilin da ya haddasa hadarin jirgin ba.
Sai dai mahukuntan sunce basu cire tsammanin cewa makami mai linzami ne ya yi karo da jirgin ba, abinda yasa ya tarwatse daga nisan mita dubu 9 da dari 4 a hamadar dake Sinai.
Wannan ne yayi dalilin mutuwar mutanen 224 dake cikin jirgin.Sai dai kawo yanzu ba’ a hakikance cewa shin injin din jirgin ne ya kone ko kuwa makami mai linzami ne yayi karo dashi ba.
Amma dai masana sun shaidawa wata kafar yada labarai na Amurka cewa shi wannan naurar hangen nesa mai hango walkiya yana iya hango hadarin jirgin dake aukuwa daga sararin samaniya, musammam abinda ya shafi fashewar bomb, ko kuma fashewar injin din jirgin dake kan tafiya, ko kuma jirgi kirar Metrojet A321 da yake kan tafiya, kai hatta wani bangaren jirgin dake tafiya idan ya tunni kasa.